ArewaKingz

No.1 Arewa Entertainment Site

☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺

SPORT: Ronaldo Yasake Shawara Gameda Barin Kungiyar Real Madrid (Karanta)
Cristiano Ronaldo ya fasa barin Kungiyar Real MadridBabban Dan wasan Duniya Cristiano Ronaldo ya fasa barin Real Kungiyar Madrid da alamu dai Tauraron ya sake shawara game da zama a Kulob din.
Rahotanni daga Jaridun Kasar Spain sun nuna cewa ‘Dan wasan zai cigaba da zama a Real Madrid bayan da ana tunanin Dan kwallon zai koma Kungiyar PSG ko ya koma kasar Ingila inda yayi suna.
Dan kwallon na Duniya zai bayyana a gaban Kotu a karshen wannan watan na Yuli domin wanke kan sa. Amma Jaridar AS tace Ronaldo ya yanke shawara zai cigaba da taka leda a Kungiyar na Real Madrid.
Kamar yadda mu ka samu labari kwanaki daga Jaridar Daily Mirror ‘Dan wasan yace dole sai Real Madrid ta biya kusan Dala Miliyan 16 da ake zargin sa da kin biya domin haraji domin ya cigaba da takawa Kungiyar leda.